Duniyar So Lyrics
- Genre:Afrobeats
- Year of Release:2021
Lyrics
Duniyar So - Auta mg boy
...
ok kashifun kiɗa
yehhh a duniyar so ke ce wacce na fi ƙauna.
zan baki komai da kike so farin ciki na
kina ta farko a cikin zuciya ki zauna
ki san nufi na, kina a raina
ke ce ruwa ke ce yunwa da ke ciki na ƴan mata
ehhhh da ka kira kalmar so sai na jini kwance
na ɗan sake sa ina zauna na hau kwatance
da Ni da kai kan so yau ga shi mun kasance
kamar amare, muna a tare
mun za ma jini da hanta yau babu mai raba mu nai fata
ehhhh da ni da ke mun saba
a so muna cin riba
matso garen yan mata ke ce abar call number
akan ki ne soyayya, na sa ta ɗamba-ɗamba
ina jiran ki a ko da yaushe farar fita mai kunya
ina ta jin dadi wanda ba misaltawa, gare ka nai komai saboda burgewa, sabida soyayya har ake makancewa, so nake ka riƙe amana kar ka bar Ni mai so na
it's amjad record
ok
kashifun kiɗa
ehhhh yarda ta bi yarda kuma kauna sai ƙauna, ba wacce nake so sai ke babu alaye
yaa zaɓin raina kai zan kaiwa iyaye,kyautar Allah ce shi yabbani masoyi
soyayya in ba taki ba ba ta a gabana, bata burge ni don ke ce naka yayi
in baka kusa na farin ciki bashi a guna duk sai na ɗimauce tamkar babu magoyi
Ni ke na fi ƙauna
ni ma kai na fi ƙauna
baiwar Allah ce yau shine ya haɗa mu