Alkawari Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2023
Lyrics
Alkawari - Auta mg boy
...
Eh alkawari damke ki rike
kar kayi wasa kar ka sake
Jin ki nake kaunarki nake
a cikin Raina kalabe
Zuciya begen ki take
kar ka damu gidanka nake
soyayyace ta hada mu
rabuwarmu akwai wahala
Eh alkawari ki rike da karfi
son ki nake kiji ba da waiba
kaima alkawari ka rike da karfi
son ka nake kaji ba da waiba
eh kaji waiba
daga nesa na fara ganinki
na yaba da irin tafiyarki
kin yi kyau da ganin murmushinki
kika tara maza kallonki
ni na fisu na zo zamu keta hazo
da ganinki nace ga kallata
kinyi kallata
za'a wayi gari kaga munyi aure
in da rabo mu rufe ta kyaure
muyi hakuri a zama mu daure
Har wata rana muna a tare
ka zama ni na zama Kai
muyi rayuwar data burge kowa
da ta burge kowa
ya soyayya ita ta hadda mu
ko mutuwa zata raba mu
in dai tazo tare zata kaimu
in dan da Hali rami daya a hada mu
Dani da ke
Dani da ke
zamu rayu sai dai a inuwa daya
shi tsadan so bai da farashi
balle ace za'a taya shi
ya wuce duk yadda ka sanshi
ko a kala babu irinshi
da Kai zanje cikin dangi
Kai na zaba muyi rayuwa
eh muyi rayuwa