Numfashina (feat. Hairat Abdullahi) Lyrics
- Genre:R&B
- Year of Release:2021
Lyrics
Numfashina (feat. Hairat Abdullahi) - Salim Smart
...
Bazan canza alkawarin mu ba komai nisan zamani
Bazan hana zuciya son ki ba dan nima ki nai da ni
Zancen in ba naki ba bani so na ji shi
Kalamin so ba naki ba bani son fitar da shi
Jinin dake gudana a jikina naka ne
Walwala ta da murana duk sana di na son ka ne
Ga zumar so ki kurba sha ki bani
Ga hannuna ka karba jani kaini
Ahh.. Numfashi na da naki bugu dai suke
Numfashi na da naka bugu dai suke
Bana fidda rai da kai zaka zamo mijina
Tunda ina da tabbacin zaka cike hakkina
Kai ɗaya zana bawa so a iya sani na
Kaima zaka ayyana idan ka kalli idona
Bazan daina sonka ba ko da nai macewa.
Ha ha ha ha ha
Bani gajiya da furta kalmar so gunki
Nayi ajiya ta wani sirri domin ki
Babu tambaya a sonki na taka mataki
Daga raina da zuciya nake son ki
Kema zo ki bayyana in zamto rikewa.
So Dan Allah shi nake maka ba yaudara ba
Inna ganka nai zumudi ma ban sani ba
Karfin sonka ya wuce mizani ka duba
Ahh taimakawa zuciya kar mu rabe
Tausaya wa rayuwata muyi zauna wa.
Numfashi naaa...