Labarina 4 Lyrics
- Genre:Soul
- Year of Release:2022
Lyrics
Labarina 4 - Salim Smart
...
Labarina
Ba ya zama nawa
In har ba ke
Tarihina
Labarina
Ba ya zama nawa
In har ba kai
Tarihina
...
Labarina bai taba cika, in har ba ke
Shalelena kaunar ki nake
Ta daban ce ke
Kece mota sauran 'yan mata kuma keke
Tazarar ku da nisa
Har abada kin shiga raina
...
Hmm... Madadin ka a raina
Babu kamar bargo da qashi
Mun zama kamar zafi da wuta
Dan yin raushi.
Matsayinka cikin raina
Ba mai iya kau dashi
Ka zama ruwa
Mai sanyaya sashin ruhi na
Labarina
Ba ya zama nawa
In har ba kai
Tarihina
..
Kwakwalwata bata tini
Kan komai saidai ke
Idan har za'a kira ni na amsawa
Sunana ke
Makwanci na qaunarki
Take bi na tai min take
Idan har na bar sonki
Ashe raina baya jikina
Hmm Labarina
Baya zama nawa
In har ba ke
Tarihina
Zan so ka ya tamkar raina
Kamar bana son kai na
A kanka ina da yakinin
Ba zaka butulce min ba
Kai min sakayyar qauna
In huce takaicin raina
Ka illata kunci inji ya bar sashi naa
Labarina, Labarina
Labarina, Labarina
Labarina, Labarina
Labarina, Labarina
Labarina
Baya zama nawa
In har ba ke
Tarihina
Labarina
Baya zama nawa
In har ba kai
Tarihina
Lyrics by Umarpharouk 08038048513