Har abada Lyrics
- Genre:Afrobeats
- Year of Release:2022
Lyrics
Har abada - Hamisu Breaker
...
Prince Production!!!
Har abada ina yabawa masoyiyaaa...
Tunda ta shigeni raina ta kewaya...
Halayyarta ba misali mai kyan niyya...
Irin nata ban gani ba...
Kullum ke nake gani a idona...
Kalamanki sun shige min raina...
Kinji amona sahiba!! kizo da kauna...
Ke zan lallaɓa muradi na raina...
Shin ya za'ai inada ke...
Kamar atafa kike a hasken haƙora...
Wane madara idonki kece na wara...
Ko kinyi fushi kinada kyau, balle harara...
Ni wannan za na mallake...
Wata alfarma nake biɗa!! Yanzu yanzu...
Ba sai anjima ba zai zamma dazu...
Kiyi na'am kawai dani, so ya wanzu...
Burina a bani ke....
Lallai so yanada daɗi da gaske...
Amma in ka samu mai ji da gaske...
Mai alƙawari tayo cikashi yanke take...
Bana son nisa da ke...
Ko kince in dakata ban tsayawa...
Sonki yanata zabura ni ban iyawa...
Da kin barni na sani ban hayewa...
Ta ya za na tsallake...
Ƙwarin gwiwa, sarewa, duka duk yana ga ke..
Ko bacci nake da na tuna ke sai in wartsake...
In zaki taimaken ki ban dama in zama dake...
Dan na gasgata samun nutsuwa dole sai dake...
It's Abdul Records....