Loading...

Download
  • Genre:Afrobeats
  • Year of Release:2021

Lyrics

Amarsu - Ali Jita

...

Amarya share hawaye bari kuka

Amarya ga kidanki kin farka

Kinga Aure shi yasa ki kin girma

Arziki ne a duniya ake nema

Inda qauna zaman gidanki ba fama

Adduah ta Allah ya kare yan gulma

Babu wai wai mijinki gashi mai girma

So da qaunah shi yasa da alfarma

Shi yana sonki kin aminta ai kema

Shimfidar fuska ta wuce ta tabarma

Sannu Amarya gidan miji akwai dadi

Kinga Amarya a zantukanmu ba kaudi

Kiji amarya kar batunmu yai fadi

Karki damu babu sidi ba sidi

Babu qarya cikin gyada akwai gardi

Mai misali kantu yake kira ridi

Naji labari a baya anka sha fama

Da magauta da tsegudidi yan gulmah

Kwanci tashi sun sallama a Yau suma

Rayuwa ce haka duniya ake fama

In fada ne nasara tana wajen kurma

Anyi Auren magauta sun sani suma

Har wa yansunsu sun shigo bukin suma

Ga ido fes a zuciya suna kuka

Ba kamanni barin sugar cikin laka

Ga haqora ga zuciya tana tuqa

Yanzu an kammale ginin ana jinka

Amarya Amarya lokaci yayi

Ke Amarya Amarya zamani yayi

Mu muna dariya wadansu na kuka

Munbi Allah su sun biyewa yan girka

Adduarmu mukeso suna biye boka

Lokaci ne kowa da lokacin sa

Zamani ne kowa da zamanin sa

Ai kamar wane kunga bata wane

Mai abin biki dan yaje biki ne

Mai karatu ganin mu malami ne

Mai kwatance ganin mu dan garine

Da kunga qura zuwa na ayari ne

Tho Arziki dai ashe jinin jiki ne

Kuma mijinki mun gane jarumi ne

So da qauna sanadin farin zama ne

Sannu Amarya Amarsu lokaci yayi

Sannu Amarya Amarsu zamani yayi

Daina kuka mijinki ba rago ba

Kuma bazai karya dukka alqawar ba

Kuma bazai sha idan baza ki sha ba

Kuma bazai bacci In idonki bai ba

Kuma bazai kwana inda babu ke ba

Yace bazai qara mikki kishiya ba

Similar Songs

+

      -   or   -

      -   or   -

      NG +234

          Please Select A Playlist

          Add New Playlist

          Share on

          Embed: Love & Light EP

          Custom Size :

          • Default
          • Desktop(300*600)
          • Mobile(300*250)

          Type :

          • HTML/HTML5 (WordPress Supported)
          Get Boomplay Premium
          for
          Payment Method
          Pay With
            Review and pay
            Order Date
            Payment Method
            Due Today
            Flutterwave
              Subscription Successful

              Congratulations! You have successfully activated Boomplay 1 Month Premium.

              Now you have access to all the features of Boomplay App.
              Payment Failed

              Please check your balance and then try again.

              You'll lose your subscription if we don't have a working payment method for your account, so please check your payment details.
              Need help? Contact Boomplay Subscription Support.
              Payment Processing...
              10 s

              Payment is being processed by . Please wait while the order is being comfirmed.

              Payment Processing
              Your order is processing, and it may take up to a few days for the service provider to handle your payment. Please kindly stay tuned and check your order status in ‘User Center’.
              About Order Status