Matata Lyrics
- Genre:Afrobeats
- Year of Release:2013
Lyrics
Matata - Ali Jita
...
Soyayya adala, Soyayya ce ruwan zuma,
Soyayya ta gari tana da dadi a zuciya.
Inama Inama, inama ya Masoyiya.
Nafisah sarauniya, Matata rabin zuciya,
Nafisah gimbiya, nafisah kece mairama
Uwar ya yana sarauniya, nafisah taka a hankali soyayya da dadi in kayi dace da sahiba soyayya da dadi in kika dace da sahibi soyayya farin ciki ce wanene bai santa ba. Soyayya mai sanya kuka sannan tasa kayi daria, ai kuka da idaniya sannan ayi kukan zuciya, ina ma ina ma ina ma ya gimbiya, Nafisah tace mijina in ba kaiba sai rijiya, Matata taurariya in ba ke ba zan sha wuya sannu mairama nafisah madubi zuciya, taho taurariya haske mai haske zuciya soyayya ruwan zuma ce in kinsha sai ki ban nasha, Kauna da tausayawa soyayya ce take sakawa , Matata kin cire tuta alkawarin da kikai rikewa mun tabbatarwa juna dani dake ba ma rabewa taka a hankali Nafisa kin zama garkuwa mai nutsuwa mai hankali mai ilimi ce ke kuwa. Nafisa sarauniya Matata rabin zuciya. Uwar ya yana gimbiya, Nafisa kece mairama, soyayya tanada dadi, in kayi dace da sahiba, ina ma ina ma ina ma ya gimbiya, Nafisa sarauniya Nafisa haske idaniya,..