Loading...

Download
  • Genre:Afrobeats
  • Year of Release:2013

Lyrics

Labarin Duniya - Ali Jita

...

Jama´a ga Ali jita Na zo zan kada yar jita ta ×2


Duniyaaa, Labarin duniya

Duniyaaa, Wayyo duniya

Zama da masoyi dadi Rabuwa da masoyi daci.

Zama da masoyi dadi ae rabuwa sam batada dadi.

Ga wata can tana ta zumudi Duniya ba´a mata kaudi.

Duniya rawar yan mata Ni tintini na manta ta Na gama gane manufarta Kai ma. malan ajiyeta Duniya kuma zancen banza.


Duniyaaa, Wayyo duniya

Duniyaaa, Labarin duniya

Wataran ina da budurwa Fara ta ke tas kyakkyawa Amma dan banida nera naga takaicin duniya.


Allah bani kudin nan nima Nayi sadaka nai kyauta Na huce takaicin zamani na.


Duniyaaa, Wayyo duniya

Yan yara ku je makaranta Musamman ma ku mata Mae ilimi ta banbanta koh dama a cikin yan mata.

Ina tausayawa matasa Dan basuda aikin komae Sai zaman kashe wando ae maula ba aiki ne ba.

A tausayawa talakawa Dan babu batada dadi Mae sa gigi da zumudi Talauci in kun gane Ba karamin ciwone bah.

Arziki daga Allah ne Nasan shine mae yin komae.

Da gari yayi wayewa Wani zaije aikin gona Wani koh shi su zaije Wani zaije turin kura Wani koh shi baya komae bashida kowa bashida komae .

Mai hakuri zai dafa dutse Ba ni ne farkon zance ba.

Sanin maza ma jari ne Ba jita ne ya fara fada ba.

Sabo da maza ma jari ne Ba ni ne farkon zance ba.

Ae arziki daga Allah ne Ba yin boka koh malam ne ba.

Sihiri baya daurewa Zancen karya ne yan mata.

Ga wani labari yan mata Ku saurara ku fahimta Labarin wata mata Burinta mallake angonta Lallae ita ta so kanta Kuma ta zalunci kanta Angonta akwae shi da hali Dan kasuwa mae hali Magidanci ne sosae ae ba karamin yaro ne ba.

Ta kai sunanshi ga boka Kasan abinka da mata Burinta a sashi ya so ta Har ma yake tsoranta Dabin duk umarninta Yaji ma bayasan kowa Bayaso yaga kowa sai ita bataso yayi nisa.

Boka yace ta samu bukata Koma gidanki ki huta A´sannu sannu asirin zai aiki amma ba da garaje bah.

Yan kwana biyu ba labari Asiri ba tasiri ta kara komawa gun boka a kara wani wancan bai hau ba.

Boka ya kara kan wancan Wanda akai ya dara wancan Koma gidanki ki huta za ki ga aiki da gaggawa.

Alhaji lamari sun rikice Bashida aiki zai zance Kasuwanci sun lalace Kullum ga shi gida kwance Dik inda tayi yana bin ta Sam baya nisantar ta Tai ta fada ya kyale ta amma baya kyale ta Shi ke tsefe gashinta Ko da gaban kawayanta zai zo ya zauna cinyarta Lamarin ya fara damunta Mijinta ya zama bawanta abu yaki ci yaki cinyewa Gaba kullum ya ka karawa Ta tai ga boka ya kwance wa Yace mata bai iya kwancewa Baya kwancewa.


Duniyaaa, Wayyo duniya

Duniyaaa, Labarin duniya

Duniyaaa, Mu guje duniya

Duniyaaa, Mu kyale rudin duniya

Duniyaaa, Mu kyale kyawun duniya

Duniyaaa, Mu kyale zancan duniya


Jama´a ga Ali jita Na zo zan kada yar jita ta ×3.

Similar Songs

+

      -   or   -

      -   or   -

      NG +234

          Please Select A Playlist

          Add New Playlist

          Share on

          Embed: Love & Light EP

          Custom Size :

          • Default
          • Desktop(300*600)
          • Mobile(300*250)

          Type :

          • HTML/HTML5 (WordPress Supported)
          Get Boomplay Premium
          for
          Payment Method
          Pay With
            Review and pay
            Order Date
            Payment Method
            Due Today
            Flutterwave
              Subscription Successful

              Congratulations! You have successfully activated Boomplay 1 Month Premium.

              Now you have access to all the features of Boomplay App.
              Payment Failed

              Please check your balance and then try again.

              You'll lose your subscription if we don't have a working payment method for your account, so please check your payment details.
              Need help? Contact Boomplay Subscription Support.
              Payment Processing...
              10 s

              Payment is being processed by . Please wait while the order is being comfirmed.

              Payment Processing
              Your order is processing, and it may take up to a few days for the service provider to handle your payment. Please kindly stay tuned and check your order status in ‘User Center’.
              About Order Status