Almukhtari Shirinka Daban Lyrics
- Genre:Afrobeats
- Year of Release:2018
Lyrics
Almukhtari Shirinka Daban - Fadar Bege
...
Almukhtari shirinka daban
Almukhtari shirinka daban
mai sama sarkin masu fada
Allah farko kai na fada
zan fadi wanda kake ta fada
za'a fade ni idan na fada
ko a ina inyi alfahari
Almukhtari shirinka daban
rabbi ilahu dakai na nutsu
son Mahmudu dashi na matsu
gun begen sa anan na nutsu
ban nutsuwa a yabon na nutsu
inyi ta zubashi kamar madadi
Almukhtari shirinka daban
salli alaihi bila adadi
ja ragamar da da aswadi
share gaba daya sha madadi
wa alihi Allah ahadi
sasu ciki da aba Bakari
Almukhtari shirinka daban
Mukhsulu zul wajhi ahlan bika ya Rasulallah
mai amsawa mai nema salatu alaika sallallah
man huwa sirru zatullah imamul ambiya'ullah
jadda kamala ainaika ahlan bika ya Rasulallah
Almukhtari shirinka daban
rabbi dada mini inyi gaba
duk ka zuba mini inyi ta zuba
in na fada aji nayi gaba
wanda yaji ta ya kara gaba
nagode maka al witri
Almukhtari shirinka daban
sannu da kyau gaibun masana
gamu gaba daya mun tsuguna
kai na sani ya malja'ana
kai na rike kuma ban izuna
wa ya tabaka ya wayi gari
Almukhtari shirinka daban
sonka kadai shine fahari
binka kawai shine lamari
kai mu kirashi uban Hashimi
shi yafi kowa alkawari
zulhu kidaru wal kadari
Almukhtari shirinka daban
dole abika ama ladabi
sarki mai dogon takobi
kogi mai wanke zunubi
sonka nake ba tararrubi
mai kauye mai cikin gari
Almukhtari shirinka daban
Jeka salamun uban cika
kai ka cikar da cika ta cika
sai da cikar ka cika ta cika
mai matsayin da yakai matuka
a sonsa Ilahu yake uzuri
Almukhtari shirinka daban
Annabi kaine babu ya kai
dole a zoma a gaida kai
kowa ya samu yaje da kai
ba'a bayarwa babu kai
wanda ya kika yana garari
Almukhtari shirinka daban
salli ala kanzul a'azam
man nuruhu nurul islam
wa ahli baitihil kiram
wa sahbihi zawwul kiram
wa awliya nurul absar
Almukhtari shirinka daban