In Zaki So Ni Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2024
Lyrics
In Zaki So Ni - Sadiq Saleh
...
a rai na da harshe da zai shaida ta
Zuciya na da kulli kar tayi min keta
Son ki ya shige ni har ya sauya fata ta
Ba ta biyun ki na fada gani hujja ta
Tsaftataccen kalma tayi
Tarbiyyar ki ina so yayi
Masu kin ki asara sun yi
Damina, bazara, ko sanyi
Komai nayi miki tuntuni kin yi
Kin fi son da nake miki girma
Komai ya kare indan zaki so ni
Ko zaki zama ajali na a barni
Komai ya kare in zaki so ni
Ko zaki zama ajali na a barni
Zan fadi da baki na
Mai yake cikin raina, zan baje miki
Za na bada komai na
Har zubin halittu na, in sadaukar miki
Na tona asirai na
Fallasa dawakai na, so nake miki
Ko iya kalamai na
Sun isar da sako na, babu shamaki
Takaici, da kunci, yaushe zasu gushe?
Watarana nakan ji kamar na fashe
Mu guje wa yan gulma, kunne mu toshe
Gasa na masoya, mune munka lashe
Na nausa, nayi nisa, yaushe zamu ishe?
Muyi tadi, mu tafa, mu kashe
Komai ya faru indan zaki so ni
Ko zaki zama ajali na a barni
Komai a kwace mini, mini, mini, mini, mini
In zaki so ni
In zaki so ni
Haka ma komai ya kare mini, mini, mini, mini, mini
In zaki so ni
In zaki so ni
Kyakkyawa ce ke
Dole in yaba so dake
In muna tare
Ban bari a tanka ki
Hadimi ne ni
Mai tsaro a fadar ki
Ko an kwankwasa kwan-kwan-kwan
Na garka me kam-kam-kam
Ko sun kai gari
Ko sun san mari
Nine jarumi, kuma nine mai kaunar ki har kullum
Komai in za'a min na yarda, na yarda
In zaki so ni
In zaki so ni