Dakin So Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2020
Lyrics
Dakin So - Nura M. Inuwa
...
Dakin So _____ Nura M Inuwa
....... Intro .......
burin raina mu zama mata da miji dakin kauna in na saka ki kar ki fito...
burin raina mun zama mata da miji dakin kauna in ka saka ni zanyi zama...
...... chorus ......
dakin so buri na masoya su shige kogin kauna kyau na masoya Kar su fito...
.....verse 1......
ka fada mini na fada maka so abinda ya kunsa
sirrikan zuciya dukan raina na bar maka fansa
Inda rai da rabo cikin so yau ina muka dosa
so nakeyi ni kaban yarda jikin ka na kwanto...
......verse 2 ......
kullum zuciya tana radadi
so ciwo ya zame mini
kaunar ki cikin jiki da jini dan Allah ki tausaya mini
kalaman so biya mini
In na manta tina mini
Ido kuka ya daina...
...... chorus ......
dakin so buri na masoya su shige kogin kauna kyau na masoya kar su fito...
....... verse 3 ........
ka rike ni na rike ka soyayya
alkawarin da mukayi ban karya
Inko ka guje ni kaga sai jinya
a gidan ka zaka bani tarbiya
In kace nace da kai da jin kunya
Inuwa akwai jikin iccen kanya
In ka samin so na sama mun cire kokwanto...
....... chorus .......
dakin so buri na masoya su shige kogin
kauna kyau na masoya Kar su fito...
........ verse 4 .........
shi so in dai ya kama mutum akwai matsala da ya fice
kamar hanta da jini hakaza rashi na ruwa ke Kar ice
Idan na rasa ki zan mace
tunani nawa zai bace
In kurbi ruwa na kauna...
........ verse 5 ........
na taho gunka Ina neman kamin alfarma bani Jin komai in ba zancen ka na zama kurma
zanji dadi in da kanka ka sani hannun dama
duk abinda kace zanayi maka shi ko zana azabtu...
........ verse 6 ........
kin dabaibayeni kin sakan sarka magana nake Ina yawan Saka
ga amana tawa tashi ki damka
so dafin sa ya wuce dafin fika
warwareni ga wuyana na mika
masu kushe so dukan su sun duka
nayi narkewa akan kaunar ki safe da rana...
....... chorus......
dakin so buri na masoya su shige kogin kauna kyau na masoya Kar su fito...
burin raina mun zama mata da miji dakin kauna in ka Saka ni zanyi zama...
........chorus........
dakin so buri na masoya su shige kogin kauna kyau na masoya Kar su fito...