Asusu na Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2023
Lyrics
IBN nee!
Hubbi na
Wayyoo, wayyoo
Baby na
Wayyoo
Zan rusa asusu na
Dan soyayyar ki
Da kin furta kalaman nan
Ehh! Masu dadin nan
Hubbi na
Wayyoo, wayyoo
Baby na
Wayyoo
Zan je ta gida in samu umma ta
Ince, ni a siyar da gado na
In hada jari na
Da adashe na
In zuba
In sadaukarwa soyayya ta
Soo, na tsunduma so
Gani a Kogin so
Zuciya ta kamu da so
Wai an ce ni na biyewa
Rudin mata
Akan ki
Sai dai a kiran bawan mata
Zan rusa asusu na
Dan soyayyar ki
Da kin furta kalaman nan
Ehh! Masu dadin nan
Hubbi na
Wayyoo, wayyoo
Baby na
Wayyoo, Wayyo
Hubbi na
San ka ya shigen rai na
Ya ratsa kwakwalwa ta
Ya nutse cikin zuciya
Ya ratsa bargo na
Da jijiyoyi na
Har jinin jiki na
Sunan ka suke ambata
Na kosa na zamo matarka
A ce, ni gani yau a dakin ka
Zan yi kwalliya kullum
In gyara gado
In jira ka Hubbi na
Har kazo ka kwanta
Zan rusa asusu na
Dan soyayyar ki
Da kin furta kalaman nan
Ehh! Masu dadin nan
Hubbi na
Wayyoo, wayyoo
Baby na
Wayyoo, Wayyo
Wayyoo, Wayyo
Wayyoo, Wayyo