Daga fadima Lyrics
- Genre:Others
- Year of Release:2024
Lyrics
Daga fadima babu kowa
Ai maganar hakkane
Inbasu ganeba mu mun gane rayuwa sai da haske
In fadima tai rubutun mai kuma atsarawa bayi
Infadima tai karatun nan kuma zamu gane masoyi
Ruhi idan ya fahimta to jasadi yana douki sanyi
Chaji cikin masu alkadarinda isarsu shinee cikake
Magana ake na tsokar kirjin mahamudu maulaklmawali
Wato uban talikai daya khairinasi ainil kamali
Sha ambato shakira madarar shaukantuwa zal wasila
Allah sallatinka wanda kakeyi mai zuhuri ahaske
Zattin da bazaya ya dou dattiba nake nufin girmamata
Ince salamun alaiki uwar daraja cikin martabata
Mai bada yanci jalila iyakar godiya shugabata
Abdallah ne mai yabo agareki da sonkune rayuwata
Daga fadima babu kowa
Inbasu ganeba mu mun gane rayuwa sai da haske
Kaunarki ta bayyanani idon nazara Nakeso uwata
Yarda da Allah cikin yardanki abun nufi fadimata
Kice wadata garaina imani dama wanzuwata
Hujjar akwai rabbana kece dan ku kuke bamu haske
.
Wallahi baza a haifi diyar da takai gwaji ko kamaba
Kinshafe motsin halitta shikenan jamili dabiba
Kin kora kowa da tabbatuwarki akan mukaminki haiba.
Yayanki sun razanasu atarrayar zuhuri aduba
Da fadinki zati yasamu jamala ga ruwa ga tufafi. .
Akayarda haske cikinku yake haske da daiyi najati
Bawanda zaisanku komai alkalami da baiwa da sauti..
Kun shafe ilimin halitta maulati natija ga aikel
Daga fadima babu kowa
Inbasu ganeba mu mun gane rayuwa sai da haske
Sashinku Allah yake duba jinkai da tsira batula
Ayabeku arabauta dacewa kune abunso akila
Sai kin agaza kin sitirta za a mutunta ayya jalila
Kunyarku nidai nakeji umma abiha haska a haske
Yau duniya tayi rauni sayyida kuyi jibintarmu hali.
Kirjinmu kar yay duhu muta siffatuwa ijaba qabuli
Kunsanmu bama iyawa saikun tallafa auwali
Kussancindai asanda tuba nayi badomin halinaba sake
Nurriya sirrin ilahiya mai tsarakake masu tsarki.
Balle hijjaban mu gana in ganar da zabi asawki.
Incewa bayi akwai wani almari a hakki da anki
Rai zai mace take inyaga ainu a hakku inkai tarraki
Daidai da kirjinka daidai ganewarka ya malamina.
Inkace isar zaka gane yadda abun yazo yau da rana.
To anjima za asawya salo kaji ka dimauce a suna
Ankarasama tunani inda kake zama ko ka kwana
Mai takurewa ajal sai ya gane mukaminki shima
Ga albishir inayamun sulukin zai mace ko ya suma
Dagana bazai sake motsawa ya yunkara ya karima
Ba asan a yaya kike buyaba da bayyanar taki aima
Dan aruga an katange sanin kowa a ganeku koli
Ba wanda zai sanku komai ji da ganisa buya da fili
Asuraru bata shiga buyarki da biciko ainu hali.
Ramzi hisabi suna aje to wazaya diba a kwali
Daga fadima babu kowa
Inbasu ganeba mu mun gane rayuwa sai da haske
Ilimai basa assasaba nakara tunawa gangar jikina
Gani bazai gane nanba fidanatu sitirar alamina
Kece anan kuma achanma ke akabaiwa yar annabina
Zara'u mumilmuhabbaty na zabeki na karya sinke
Kyauta nakeso kimun na fahimtar waridin zuciyata
Insamu harshen da ke magana yayi daiyu izaya furta
Ayimun gwalagwalan ma'anona atassarifin rayuwata
Nasan jalala mabudice ta ganin jamala atake
Burin dai rai keta fata tai muku so ilallahi umma
Ameeen aban arzikin faila inrayu bana nadama
Komai wuyi tayi dadi soyayyarku ce ai alama
Shaida mukaiwa masoya dacewa salamun salima
Daga fadima babu kowa
Inbasu ganeba mu mun gane rayuwa sai da haske