Farkon Mafadi Lyrics
- Genre:Afropop
- Year of Release:2017
Lyrics
Farkon Mafadi - Fadar Bege
...
Farkon mafadi karatu ne a saman ilimi sai mai ruhin soyayya shine zai gane zance na (×2)
komai zan fara dakai nake son somawa Rabbana babban sarki ki nake kuma godewa karamin hikima da kokari gun rerawa alfarmar bushra sayyadina gausul agawasu maulana.
Subhanaka ya Allah dado dubu na salatin ka ya tabbata gun sarki mai shiga a kadaitar ka da alaye har sahabai 'yan gida nasa tsarkaka kamar sheick Tijjani da Jiyali har Barhama Baye maulana.
Sannu dashan fama ya faman ka da 'yan maula kmar Fadar Bege wanda yazo maka ba hula ga wata na dauko ga daya can na kai talla baba a kar min in ta fada ba kosawa ga ma'aiki na.
wata rana ce ta laraba ko da sassafe sai naji an doko gida nace waye a tafe da buwar kofa shi na gni yayi yo yafe Hafiz Abdallah mai yabo ga Muhammadu Daha maulana.
Na gama budewa ya rungume ni yna cewa a abunda yake ta fada cikinsa yana kuma rantsewa yana Fadar Bage wallahi ka gama dacewa nace masa kai mu shigo gida ka bani batun lamari na maula na.
Shigar mu cikin daki ba wuya muka zazzauna nace masa ya Hafiz bani duk labari na yace Fadar Bege daren jiya kafin tashi na naga Rasulallah abun fadi sirrul asraru maulana.
Take na gyara zama bai gushe ba yana cewa mursalai ne dari uku a cikin su da karawa ga malakai a sama cikin su ba mai haskawa ga kujerar gwal a sama ana jiran saukar Mahamudu maulana.