Duniya Lyrics
- Genre:Afrobeats
- Year of Release:2023
Lyrics
Duniya - Auta Mg Boy
...
A MG Boy record
Allah, alhamdulilahi Allah
Allah, alhamdulilahi Allah
Alhamdulilahi Allah
Eh mana
Allah, alhamdulilahi
Alhamdulilahi Allah
Allah duk abunda zan samu nai imani kai kake bani Allah
Duka ci na, da abunda zan sha hada sutura nai godiya gun ka Allah
Haka nan wata rana zan tashi banda ko sisi wanan hikima ce ga Allah
Allah kafi mu tausan mu (Allah)
Ka jikan iyayen mu (Allah)
Ka hada abokan mu (Allah)
In tamu tazo kasa rahamarka ta lulube mu gaba daya
Allah, alhamdulilahi (Allah)
Alhamdulilahi (Allah)
Alhamdulilahi (Allah)
Alhamdulilahi (Allah)
Alhamdulilahi (Allah)
Alhamdulilahi (Allah)
Alhamdulilahi Allah
Duniya makaranta ce mutanen mu
Wani na nema wani gashi ya samu
Wani sai yayai faskare yake samu
Wani na ofis zaune yake samu
Wani ko sai yayai tuki yake samu
Ga wani shi sai roka yake samu
Mu gashi a waka ne muke samu
A hakan wasu kuma suke ta kyamar mu
In suka gane mu su dinga kyarar mu
Allan da yayi ku shine yayi mu
Toh ku dinga tinawa kaddarar kowa
Allah shine yasan gaibu
Allah, alhamdulilahi (Allah)
Alhamdulilahi (Allah)
Alhamdulilahi (Allah)
Alhamdulilahi
Alhamdulilahi
Duk abunda kakeyi kaso masoyonka dan shine sabo na alkairi
Shi ko makiyi wanan masheki ne karka sake ka mai rikon sirri
Ka yarda da Allah shi yake yi komai yunwa sai kaci garri
Abunda ka samu shine naka
Rabonka bazai wuce ka
Ka kama ubangijin ka
Shine mai daukakar ka
In dai duniya ce gamu cikin ta munata labari
Kadan da kadan sai ta shude kasar nan sai tazama tarihi
Ka aikata alkairi a yau goben ka tayo kyau tsarkake ruhi
Ka bar munafurci
Kar kayo sata
Kar kayo caca
Kar kayo shirka
Kar kayo gulma
Karka fara ha'inci
Babu zanba
Ba zama da zalunci
Hakkin kowa sauke a kanka ka huta
Fuskanci ubangiji, ka nemi albarka
Salamun'aiki ya umma mamana mai sani kan hanya
Inda nai yi kure kina kirana ki min gyra, gyra na tarbiya
Umma na gode kinyi min komai Allah yayi miki sakaiya
Babana kaine duniya ta
Idan nayi waka sai ka yaba ta
Ka samin albarka ina alfahar da iyaye na masoya ne
Allah, alhamdulilahi naga iyaye na a duniya
Wani tunda yazo bai san iyayen shi ba
Domin basu raye
Allah ka jikansu ka gafarta
Alhamdulilahi Allah