Loading...

Download
  • Genre:Others
  • Year of Release:2015

Lyrics

Luke 02 - Audio Bible

...

A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da suke ƙarƙashin mulkinsa. 2 Wannan shi ne ƙirga na fari da aka yi a zamanin Kiriniyas, mai mulkin ƙasar Suriya. 3Kowa sai ya tafi garinsu a rubuta shi. 4 Yusufu shi ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa), 5don a rubuta shi, duk da Maryamu tashinsa, wadda take kuma da ciki. 6Sa'ad da suke can kuwa, sai lokacin haihuwarta ya yi. 7Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufi shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani komi dabbobi, don ba su sami ɗaki a masaukin ba.


Makiyaya da Mala'iku

8A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare. 9 Sai ga wani mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewayensu, har suka tsorata gaya, 10 Sai mala'ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane. 11 Domin yau an haifa muku Mai Ceto a birnin Dawuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji. 12 Ga alamar da za ku gani, za ku sami jariri rufe da zanen goyo, kwance a komin dabbobi.” 13Ba labari sai ga taron rundunar Sama tare da mala'ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa,


14 “Ɗaukaka ga Allah ta tabbata, can cikin Sama mafi ɗaukaka.


A duniya salama ta tabbata, ga mutanen da yake murna da su matuƙa.”


15Da mala'iku suka tafi daga gare su suka koma Sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu tafi Baitalami yanzu, mu ga abin nan da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar da mu.” 16Sai suka tafi da hanzari, suka sami Maryamu da Yusufu, da kuma jaririn kwance a komin dabbobi. 17Da suka gan shi, suka bayyana maganar da aka faɗa musu game da wannan ɗan yaro. 18Duk waɗanda suka ji kuma, suka yi ta al'ajabin abin da makiyayan nan suka faɗa musu. 19 Maryamu kuwa sai ta riƙe duk abubuwan da aka faɗa, tana biya su a zuci. 20 Makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah, suna yabonsa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.

see lyrics >>

Listen to Audio Bible Luke 02 MP3 song. Luke 02 song from album Hausa New Testament is released in 2015. The duration of song is 00:06:36. The song is sung by Audio Bible.

Related Tags: Luke 02, Luke 02 song, Luke 02 MP3 song, Luke 02 MP3, download Luke 02 song, Luke 02 song, Hausa New Testament Luke 02 song, Luke 02 song by Audio Bible, Luke 02 song download, download Luke 02 MP3 song

Comments (0)

0/500

    New Comments0

    What do you think of this song?

    +

        -   or   -

        -   or   -

        NG +234

            Please Select A Playlist

            Add New Playlist

            Share on

            Embed: Love & Light EP

            Custom Size :

            • Default
            • Desktop(300*600)
            • Mobile(300*250)

            Type :

            • HTML/HTML5 (WordPress Supported)
            Get Boomplay Premium
            for
            Payment Method
            Pay With
              Review and pay
              Order Date
              Payment Method
              Due Today
              Flutterwave
                Subscription Successful

                Congratulations! You have successfully activated Boomplay 1 Month Premium.

                Now you have access to all the features of Boomplay App.
                Payment Failed

                Please check your balance and then try again.

                You'll lose your subscription if we don't have a working payment method for your account, so please check your payment details.
                Need help? Contact Boomplay Subscription Support.
                Payment Processing...
                10 s

                Payment is being processed by . Please wait while the order is being comfirmed.

                Payment Processing
                Your order is processing, and it may take up to a few days for the service provider to handle your payment. Please kindly stay tuned and check your order status in ‘User Center’.
                About Order Status